Kamfanin dillancin labaran Afri-Gate News ya rawaito daga majiyoyin labarai na cikin kasar Morocco suna bayyana haka. Sun kuma kara da cewa gwamnatin kasar Morocco zata aike da sojojinta na musamman kimani 1500 zuwa kasar Saudia da farko sannan daga can rundunar hadin guiwa na kasashen Larabawa karkashin jagorancin kasar saudia zata yi jigilarsu zuwa kasar Yemen don tallafawa kasashen maida Abdurabbu Hadi Mansur tsohon shugaban kasar na Yemen kan kujerar shugabancin kasar da karfi.
Idan ba a’ manta ba Tun watan Maris da ya gabata ne kasar Saudiya da kawayenta suka fara kaiwa gwamnatin kasar Yemen hare hare ta sama , amma daga baya sun fara aike da sojojin kasa don kammala wannan aniyar tasu.288